Header Ads

  • AN SAWA SABUWAR MAKARANTA SUNAN MATAR SHUGABAN KASA

    A ranar Talatar da ta gabata aka kaddamar da sabuwar makarantar firamare a garin Maiduguri,inda aka sanyawa makarantar sunan uwar gidan shugaban kasa wato Hajiya A'isha Buhari.
    Makarantar wadda gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Alh. Kashim Shettima ta gina ta samu budewa ne daga tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyya mai mulki ta APC, wato Alh. Ahmad Bola Tinubu. Wannan ya faru ne a kokarin da gwamnati keyi na farfado da harkar ilimi a jihar data samu tabarbarewa sakamakon rikicin boko haram.

    No comments

    Post Bottom Ad